Nazarin Salon Mutuntarwa a Cikin Littafin Gandun Dabbobi Na George Orwell Wanda Bala Abdullahi Funtua Ya Fassara Zuwa Hausa
Student: Zaliha Ibrahim (Project, 2025)
Department of Hausa
Taraba State University, Jalingo, Taraba State
Abstract
TSAKURE Wannan binciken mai suna “Nazarin Salon Mutuntarwa a cikin Littafin Gandun Dabbobi na George Orwell wanda Bala Abdullahi Funtua ya fassara zuwa Hausa”. Nazari ne da ya shafi salo wato ɓangare na adabi wanda ya ke dubi kan dabaru da hikima da marubuta ko mawallafa ke amfani da shi wajen isar da saƙonsu. Ganin haka ne wannan aikin ya yi nazari don a gano wasu daga cikin salo da ake samu wajen amfani da siffofi na mutane ga dabbobi a matsayin hanyar isar da saƙo ga al’umma. Wannan binciken ya taƙaita ne kacokan a Littafin Gandun Dabbobi.. An raba wannan aikin zuwa babi biyar. Kuma an kawo ra’o’i guda biyu waɗanda suka haɗa da: ra’in sigar adabi wato (structural analysis) da ra'in tsaranci (structuralism). Sannan daga ƙarshe aka ɗora wannan aiki a kan ra'in rain sigar adabi structural analysis domin shi yake da nasaba kuma ya fi dacewa da wannan aikin domin ana nazari kuma ɗora kan abin da ya shafi zube da waƙa da wasan kwaikwayo. An tattara bayanai ta hanyar karance littafin. An jero wurare da mawallafin ya yi amfani da salon mutuntarwa a cikin littafin. Daga ƙarshe Binciken ya gano irin salon mutuntarwa da mawallafin ya yi amfani da shi a cikin littafin inda ya ba wa kowane matsayi da kuma iyaka da zai tsaya a cikin littafin. Har ila yau ya gano irin rawar da kowace dabba ke gudanar a cikin littafin.
Keywords
For the full publication, please contact the author directly at: izaliha2020@gmail.com
Filters
Institutions
- Abdul-Gusau Polytechnic, Talata-Mafara, Zamfara State 3
- Abia State Polytechnic, Aba, Abia State 24
- Abia State University, Uturu, Abia State 71
- Abraham Adesanya Polytechnic, Ijebu-Igbo, Ogun State 3
- Abubakar Tafawa Balewa University, Bauchi, Bauchi State 15
- Abubakar Tatari Ali Polytechnic, Bauchi State. (affiliated To Atbu Bauchi) 1
- Achievers University, Owo, Ondo State 6
- Adamawa State University, Mubi, Adamawa State 8
- Adekunle Ajasin University, Akungba-Akoko, Ondo State 26
- Adeleke University, Ede, Osun State 1