"fassarar Wani ɓangare Daga Cikin “as-Sunan Al-Kubrā” Na Imām Al-Bayhaqī"

Student: Maryam Umar Aliyu (Project, 2025)
Department of Islamic Studies
Bayero University, Kano, Kano State


Abstract

Abstract Wannan bincike yana nazari ne kan fassarar wani ɓangare daga cikin sanannen littafi na hadisi mai suna As-Sunan al-Kubrā, wanda Imām Abū Bakr Aḥmad ibn al-Ḥusayn al-Bayhaqī ya rubuta. Manufar wannan aikin ita ce domin fahimtar ma’anoni da hikimomin da ke cikin hadisai da wannan ɓangare ya ƙunsa, tare da fassara su zuwa harshen Hausa don sauƙaƙa fahimtar ɗalibai da masu karatu. Binciken ya yi amfani da hanyoyin nazarin turanci da fassarar kalmomi bisa ƙa’idojin ilimin fassara na addinin Musulunci. An gano cewa As-Sunan al-Kubrā na ɗaya daga cikin manyan tushe na hadisi da suka taimaka wajen ƙarfafa ilimin fiƙihu da shari’a. A ƙarshe, binciken ya nuna muhimmancin fassarar littattafan addini zuwa harshen da jama’a ke fahimta don yada ilimi da tabbatar da sahihin fahimta.

Keywords
fassarar angare cikin as-sunan al-kubr al-bayhaq